Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi*, kuma ya ce: «‌Lallai su basa tsarkakewa».

Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi*, kuma ya ce: «‌Lallai su basa tsarkakewa».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi, kuma ya ce: «‌Lallai su basa tsarkakewa».

[Ingantacce ne] [Al-Dar Al-Kutni Ya Rawaito shi]

الشرح

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya biya buƙatarsa na fitsari ne ko bahaya ya yi tsarkin hoge da ƙashin dabbobi ko torosonsa da busassun torosonsa; kuma ya ce: Lallai su basa kawar da najasa, kuma ba'a tsarkaka daga garesu.

فوائد الحديث

Bayanin wasu daga cikin ladubban bayan gida da kuma tsarki.

Hani daga tsarkin hoge da toroson dabbobi; domin cewa shi: Kodai ya zama najasa, ko kuma domin cewa shi abincin dabbobin aljanu ne.

Hani akan yin tsarkin hoge da ƙashi; domin cewa shi kodai najasa ne, ko kuma domin abincin aljanu ne su da kansu.

التصنيفات

Ladaban biyan bukata