إعدادات العرض
«Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi».
«Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi».
Daga Zubair ɗan Awwam - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Tiếng Việt Português Magyar ქართული Kiswahili සිංහල Română অসমীয়া ไทยالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum ɗaya daga cikin mutane ya yi aiki kowane irin aiki ne koda zai ɗauki igiya ne, ya tattara itatuwa a gadan bayansa sai ya saida shi ya ci daga gare shi, ko ya yi sadaka da shi ya wadata daga mutane da shi kuma ya kare fuskarsa daga ƙasƙancin roƙo; shi ne ya fiye masa alheri daga ya tambayi mutane su ba shi ko su hanashi, roƙon mutane ƙasƙanci ne, mumini kuwa maɗaukaki ne ba ƙasƙantacce ba ne.فوائد الحديث
Kwaɗaitarwa akan kamewa daga roƙo da kuma tsarkaka daga gare shi.
Kwaɗaitarwa akan aiki dan samun arziƙi, koda an jarrabi baligi da ƙaramar sana'a wulaƙantacciya a idanuwan mutane.
Yaƙar da Musulunci yake yi wa roƙo; saboda haka ya wajabta yin aiki, ko da mai wahala ne; kamar saran ita ce misali.
Roƙo ba ya halatta tare da iko akan aiki da kuma neman arziƙi.
Roƙon sarki (shugaba) idan akwai buƙata ya halatta, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Haka kuma babu (laifi) a kan waɗanda idan sun zo maka don ka basu abin hawa sai ka ce: "Bani da abin hawan da zan baku," sai suka juya idanuwansu suna kwararar da hawaye don baƙin cikin ba su sami abinda zasu ciyar ba}.
[Al-Taubah: 92].
Wanda yake da larurar roƙo da kuma rauni akan neman kuɗi to ya halatta gare shi ya yi roƙo, amma kada ya yi naci, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Basa nacin roƙon mutane} [Al-Baƙara: 273].
Nawawi ya ce: A cikinsa akwai: Kwaɗaitarwa akan sadaka, da kuma ci daga aikin hannunsa, da neman halal.
التصنيفات
Kasuwanci