Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tura wani mutum akan Zakkar Banu Sulaim, ana kiransa Ibnul Lutbiyyah, lokacin da ya zo sai ya yi masa lissafi, sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyauta ce. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya…

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tura wani mutum akan Zakkar Banu Sulaim, ana kiransa Ibnul Lutbiyyah, lokacin da ya zo sai ya yi masa lissafi, sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyauta ce. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Shin me yasa ba zaka zauna a cikin gidan babanka da babarka ba, har kyautar taka ta zo maka, idan kai mai gaskiya ne». Sannan ya yi mana huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi maSa yabo, sannan ya ce: «‌Bayan haka, lallai cewa ni ina ɗorawa mutum daga cikinku wani aiki daga abinda Allah Ya jiɓinta mini, sai ya zo sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyautar da aka bani ce, shin yanzu ba ya zauna a gidan babansa da babarsa ba har sai kyautar tasa ta zo masa !, @Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar lahira*, lallai cewa na san wani daga cikinku ya gamu da Allah yana ɗauke da raƙuminsa yana kuka, ko saniya tana kuka, ko akuya yana kuka» Sannan ya ɗaga hannunsa har sai da aka ga farin hammatarsa, yana cewa: «‌Ya Allah shin na isar ?» Ganin idona da kuma jin kunnena.

Daga Abu Humaid al-Sa'idi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tura wani mutum akan Zakkar Banu Sulaim, ana kiransa Ibnul Lutbiyyah, lokacin da ya zo sai ya yi masa lissafi, sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyauta ce. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Shin me yasa ba zaka zauna a cikin gidan babanka da babarka ba, har kyautar taka ta zo maka, idan kai mai gaskiya ne». Sannan ya yi mana huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi maSa yabo, sannan ya ce: «‌Bayan haka, lallai cewa ni ina ɗorawa mutum daga cikinku wani aiki daga abinda Allah Ya jiɓinta mini, sai ya zo sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyautar da aka bani ce, shin yanzu ba ya zauna a gidan babansa da babarsa ba har sai kyautar tasa ta zo masa !, Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar lahira, lallai cewa na san wani daga cikinku ya gamu da Allah yana ɗauke da raƙuminsa yana kuka, ko saniya tana kuka, ko akuya yana kuka» Sannan ya ɗaga hannunsa har sai da aka ga farin hammatarsa, yana cewa: «‌Ya Allah shin na isar ?» Ganin idona da kuma jin kunnena.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗorawa wani mutum aiki ana ce masa: Ibnul Lutbiyyah, shi ne aikin tattaro zakka daga ƙabilar Banu Sulaim, lokacin da ya dawo Madina sai ya yi masa bayani akan abinda ya karɓa da kuma abinda ya yi amfani da shi, sai Ibnul Lutbiyyah ya ce: Wannan dukiyarku ce wacce na tattarota ta zakka, wannan dukiyar kuma anbani kyautarta ne. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Shin ba zaka zauna acikin gidan babanka da babarka ba ka duba ka gani shin za’a baka kyautar idan kai mai gaskiya ne; domin cewa haƙƙoƙin da ka yi aiki saboda su sune sababin baka kyauta, kuma da a ce ka zauna a cikin gidanka da ba'a baka kyautar komai ba, dan haka ba ya kamata gareka ka halartata saboda kawai ta sameka ta hanyar kyauta. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya hau minbari yana mai yin huɗuba alhali shi yana mai fushi, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi, sannan ya ce: Bayan haka lallai ni ina ɗorawa ɗayanku aiki akan abinda Allah Ya sanya mini tasarrufi a cikinsa na zakka da kuma ganimomi, sai wanda ya yi aikin ya zo, ya ce: Wannan naku ne wannan kuma kyauta ce da aka bani! Shin ba ya zauna a cikin gidan babansa da babarsa ba har kyautarsa ta zo masa, wallahi wani ba zai ɗauki wani abu ba daga abinda aka ba shi, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar alƙiyama akan wuyansa, idan abinda ya ɗauka raƙumi ne yana kukan raƙuma, ko saniya ce da take irin kukan shanu, ko akuya ce da take irin kukan akuyoyi. Sannan ya ɗaga hannayensa sosai har waɗanda ke zaune suka ga farin hammatarsa, sannan ya ce: Ya Allah na isar musu da hukuncin Allah. Sannan Abu Humaid al-Sa'idi - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa: Wannan abinda idona ya gani ne kuma kunnena ya ji shi.

فوائد الحديث

Shugaba ya bayyanawa ma'aikatan dake tare da shi abin da ake nema daga garesu da kuma abinda aka hanasu a cikin ayyukansu.

Narko ga wanda yake karbar dukiyoyin mutane akan zalinci.

Babu wani azzalimi sai ya zo da abinda ya yi zalincin da shi a ranar alƙiyama.

Wajibi akan ma'aikaci a cikin kowane aiki daga cikin ayyukan daula (ƙasa) ya bada abinda aka wakilta shi a kansa, ba ya halatta gare shi ya karɓi kyautukan abinda yake rataye da aikinsa, idan kuma ya karɓa to ya maida su baitul mali, ba ya halatta gare shi ya ɗaukarwa kansa su, kuma domin cewa su tsani ne na sharri da kuma ɓata amana.

Ibnu Baɗɗal ya ce: Hadisin ya yi nuni akan cewa yi wa ma'aikaci kyauta yana kasancewa ne dan godewa aikin alherinsa ne, ko dan nuna soyayya gare shi, ko dan kwaɗayin abinda ya sanya shi na haƙƙi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi nuni zuwa cewa shi kamar ɗaya ne daga cikin musulmai a cikin abinda aka ba shi kyautar, ba shi da wani fifiko akansa a cikinsa, kuma shi ba ya halatta ya mallake shi.

Nawawi ya ce: A cikin wannan hadisin akwai: Bayanin cewa kyautar ma'aikata haramun ce, kuma satar kayan ganima ne; domin cewa shi ya yi ha'inci a cikin shugabancinsa da kuma amanarsa, saboda haka ne a cikin hadisin aka ambaci uƙubarsa da kuma ɗaukar abinda aka ba shi kyautar a ranar alƙiyama, kamar yadda aka ambaci irinsa a kan wanda ya saci ganima, haƙiƙa (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi a cikin hadisin ya bayyana sababin haramta kyautar a kansa, kuma cewa ita da sababin shuganacin ce, saɓanin kyautar wanda ba ma'aikaci ba, ita mustahabbi ce.

Ibnul Munir ya ce: Za'a fahimta daga faɗinsa; "Shin ba ya zauna a cikin gidan babansa da babarsa ba" halaccin karɓar kyauta daga wanda ya kasance yana ba shi kyauta kafin hakan. Ibnu Hajar ya ce: ba ya ɓoyuwa cewa bigiren hakan idan bai ƙaru akan al'ada ba.

Usulubin Annabi a cikin nasiha shi ne gamewa ba wai yayatawa ba.

Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai halaccin yi wa wanda aka bawa amana hisabi.

Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai halaccin kwaɓar wanda ya yi kuskure.

An so ɗaga hannaye a cikin addu'a.

التصنيفات

Baiwa da Kyauta, Abubuwan da suka Wajaba kan Shugaba