إعدادات العرض
«Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala, da tsoro da rowa, da tsufa, da azabar ƙabari, ya Allah Ka baiwa raina tsoranta, Ka tsarkaketa, Kai ne mafificin Mai tsarkaketa, Kai ne majiɓincin lamarinta kuma shugabanta, Ya Allah ina neman tsarinKa daga ilimin da ba shi da amfani, da…
«Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala, da tsoro da rowa, da tsufa, da azabar ƙabari, ya Allah Ka baiwa raina tsoranta, Ka tsarkaketa, Kai ne mafificin Mai tsarkaketa, Kai ne majiɓincin lamarinta kuma shugabanta, Ya Allah ina neman tsarinKa daga ilimin da ba shi da amfani, da zuciyar da bata risina, da zuciyar da ba ta ƙoshi, da addu'ar da ba'a amsarta ».
Daga Zaid Dan Arƙam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ba zan faɗa muku (komai ba) sai kamar yadda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana faɗa: Ya kasance yana cewa: «Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala, da tsoro da rowa, da tsufa, da azabar ƙabari, ya Allah Ka baiwa raina tsoranta, Ka tsarkaketa, Kai ne mafificin Mai tsarkaketa, Kai ne majiɓincin lamarinta kuma shugabanta, Ya Allah ina neman tsarinKa daga ilimin da ba shi da amfani, da zuciyar da bata risina, da zuciyar da ba ta ƙoshi, da addu'ar da ba'a amsarta ».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी සිංහල Kurdî Tiếng Việt Magyar ქართული Kiswahili Română অসমীয়া ไทยالشرح
Ya kasance daga cikin addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - «Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa» da fakewa gareKa, «Daga gajiyawa» rashin iko akan dabara mai amfani, «Da kasala» rashin samuwar niyyar yin aiki, gajiyayye ba ya iya yin wata dabara, mai kasala kuwa ba ta ma nufinta. «Da tsoro» ta hanyar hanuwa daga gabatowa akan abinda aikata shi yake kamata, «Da rowa» da hana abinda bada shi yake wajaba, «Da tsufa» yawan shekarun da zai kai zuwa ga raunin jiki, «Da azabar ƙabari» Da sabubban da suke kaiwa zuwa ga hakan. «Ya Allah Ka bawa raina» Ka bata kuma Ka datar da ita ga «Tsron Allahnta» da aikata ɗa'a da barin saɓo, «Ka tsarkaketa» Ka tsarkaketa daga ƙasƙanci da munanan ɗabi'u, «Kaine mafi alherin wanda Ya tsarkaketa» babu wani mai tsarkaketa inbaKai ba, «Kaine majiɓincinta» Mai taimakonta kuma mai tsaya mata, «Kuma shugabanta» Mai jiɓintar al'amuranta, kuma Ubangijinta Mamallakinta kuma Mai ni'imtar da ita. «Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa daga ilimin da ba shi da amfani», kamar ilimin taurari da bokanci da tsafi, ko wanda ba zai yi amfani a lahira ba, ko ilimin da ba za’a yi aiki da shi ba, «Da zuciyar da bata risinawa» gareKa, kuma bata ƙanƙar da kai, kuma bata nutsuwa, bata nutsuwa saboda ambatanKa, «Da ran da baya ƙoshi» ba ya wadatuwa da abinda Allah Ya ba shi kuma Ya azurta shi daga halal mai tsarki, «Da addu'a» abar juyarwa «wacce ba'a amsa mata».فوائد الحديث
An so neman tsari daga waɗannan al'amuran, waɗanda aka ambata a cikin hadisin.
Kwaɗaitarwa akan tsoron Allah da yaɗa ilimi da kuma aiki da shi.
Ilimi mai amfani shi ne wanda yake tsarkake zuciya kuma yake haifar mata da tsoron Ubangiji - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, sai ya yi naso daga gareta zuwa saurin gaɓoɓi.
Zuciya mai tsoron Allah ita ce wacce take jin tsoro, kuma take raurawa a lokacin ambatan Allah sannan ta tausasa ta kuma natsu.
Zargin kwaɗayin duniya da rashin ƙoshi daga sha'awowinta da abubuwan jin daɗinta, saboda haka zuciya mai zari mai kwaɗayi akan jin daɗin duniya ita ce mafi ƙiyayyar mutum, saboda haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga gareta.
Yana kamata ga mutum ya rabu da sabubban kin karbar add'a da kuma rashin karɓuwarta.
Nawawi ya ce: Wannan hadisin da waninsa na addu'o'in da aka yi wa saja'i dalili ne akan abinda malamai suka faɗa; cewa saja'in da aka zarga a cikin addu'a shi ne wanda ake ɗorawa kai, domin cewa shi yana tafiyar da khushu'i da ƙanƙar da kai da kuma ikhlasi, kuma yana shagaltarwa daga tawali'u da buƙatuwa da kuma kakkaɓar zuciya, amma abinda ya samu ba tare da matsawa kaiba, ba kuma tare da aiwatar da tinani dan cikar fasaha ba da kuma makamancin haka, ko wanda aka haddace to babu laifi da shi, kai yana ma da kyau.
التصنيفات
Addu’o’I da aka samu daga Annabi