«‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku»*, sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai Allah da mala'ikunSa da waɗanda ke sammai da ƙassai har tururuwa a cikin raminta kai har kifi suna addu'a ta alheri ga wanda yake…

«‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku»*, sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai Allah da mala'ikunSa da waɗanda ke sammai da ƙassai har tururuwa a cikin raminta kai har kifi suna addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane alheri».

Daga Abu Umama al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An ambatawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane biyu ɗayansu mai ibada ne ɗayan kuma malami ne, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku», sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai Allah da mala'ikunSa da waɗanda ke sammai da ƙassai har tururuwa a cikin raminta kai har kifi suna addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane alheri».

[Hasan ne ta wani Sanadin] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

An ambatawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane biyu ɗayansu mai ibada ne, ɗayan kuma malamai ne, wanene yafi a cikinsu? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Falalar masanain ilimummukan shari'a mai yin aiki da su kuma mai koyar da su akan mai yin ibada wanda ya kaɗaita ga ibada tare da da cewa ya san abinda ya wajaba akansa na ilimi kamar falalarsa ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma ɗaukakarsa akan mafi koma baya daga cikin sahabbai Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana sababin hakan da cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, da mala'ikunSa cikin maɗauka al'arshi, da waɗanda ke cikin sammai na sauran mala'iku, da ma'abota ƙasa na aljanu da mutane da dukkanin dabbobi, har tururuwa a gidanta a cikin ƙasa, har kifin da ke cikin kogi; dan ya haɗa dabbobin sarari (tudu) da kogi, dukkanin waɗannan sunayin addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane ilimummukan Addinin da a cikinsu akwai tsiran mutane da kuma rabautarsu.

فوائد الحديث

Daga cikin usuluban kira zuwa ga Allah akwai kwaɗaitarwa da kuma buga misalai.

Girman ɗaukakar malaman da suka koyi ilimi kuma suka tsaya da haƙƙinsa na aiki da kuma da'awa.

Kwaɗaitarwa akan girmama malamai da ɗaliban ilimi da kuma yi musu addu'a.

Kwaɗaitarwa akan koyar da mutane alheri; domin shi ne sababin tsirarsu da kuma azirtarsu.

التصنيفات

Falalar Ilimi