إعدادات العرض
Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari, sai muka san imani kafin mu koyi alƙur'ani, sannan muka koyi alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi
Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari, sai muka san imani kafin mu koyi alƙur'ani, sannan muka koyi alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi
Daga Jundub Ibnu Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari, sai muka san imani kafin mu koyi alƙur'ani, sannan muka koyi alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.
[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya ruwaito shi]
الترجمة
العربية Português دری Македонски Tiếng Việt Magyar ქართული Indonesia বাংলা Kurdî ไทย অসমীয়া Nederlands ਪੰਜਾਬੀ Kiswahili Tagalog ភាសាខ្មែរ English ગુજરાતી සිංහල Русский मराठी മലയാളം ಕನ್ನಡ Српски Türkçeالشرح
Jundub ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari mun kusa balaga, ƙarfafa masu tsananin ƙarfi, sai muka san imani a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin mu koyi Alƙur'ani, sannan muka koyi Alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.فوائد الحديث
Bayanin cewa imani yana ƙaruwa kuma yana raguwa.
Jeranta abin da ya fi kamata a lokacin tarbiyyar mai tasowa, da kuma kwaɗayi akan cika musu imani.
Alƙur'ani yana ƙara imani, kuma zuciya tana haskaka da shi, kuma ƙirji yana buɗewa da shi.
