"Wanda ya riƙi wani kare saidai karen farauta ko kiwo ƙiradi biyu zai ragu daga aikinsa kowace rana"*, Salim ya ce: Abu Huraira ya kasance yana cewa: "Ko karen noma", kuma ya kasance manomi ne.

"Wanda ya riƙi wani kare saidai karen farauta ko kiwo ƙiradi biyu zai ragu daga aikinsa kowace rana"*, Salim ya ce: Abu Huraira ya kasance yana cewa: "Ko karen noma", kuma ya kasance manomi ne.

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya riƙi wani kare saidai karen farauta ko kiwo ƙiradi biyu zai ragu daga aikinsa kowace rana", Salim ya ce: Abu Huraira ya kasance yana cewa: "Ko karen noma", kuma ya kasance manomi ne.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga riƙon karnuka, saidai dan buƙatar farauta, ko gadin dabbobi da shuka, wanda ya riƙe kare ga wanin haka kowace rana ƙiraɗi biyu zai ragu daga ladan aikinsa; kuma shi wani gwargwado ne sananne a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.

فوائد الحديث

Ba ya halatta ga musulmi ya riƙi kare, sai dai abinda aka togance.

Hana riƙon karnuka; dan abinda ke cikinsu na ɓarnace-ɓarnace da cutukka masu yawa, haƙiƙa ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa mala'iku ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai kare; dan kuma abinda ke cikinsa na najasa mai kauri wacce babu abinda ke gusar da ita sai maimaita wankewar da ruwa da kuma turɓaya.

التصنيفات

Farauta