إعدادات العرض
Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba, sai ga miji wata huɗu da kwana goma
Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba, sai ga miji wata huɗu da kwana goma
Daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba, sai ga miji wata huɗu da kwana goma, kuma kada ta sanya tufa rinanniya sai tufa na asb (wasu tufafi ne na Yaman masu fari da baƙi), kuma kada ta sa kwalli, kuma kada ta shafa tirare sai dai idan ta yi tsarki sai ta shafa wani gutsire na tiraren ƙusɗ ko azfar».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Português Kurdî Tiếng Việt Magyar ქართული Kiswahili සිංහල Română অসমীয়া ไทย मराठी دری አማርኛ ភាសាខ្មែរالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani ga mai idda (takaba) daga barin ado na tirare da kwalli da kayan ado da kyawawan kayan sawa ga mamaci sama da kwana uku, uba ne ko ɗan'uwa ko ɗa ko wasunsu, sai ga miji kawai wata huɗu da kwana goma, kuma alokacin iddarta (takaba) ga miji, kar ta sanya dukkanin rinannun tufafi dan yin ado sai tufafin asb, shi ne tufa na Yaman wanda ake rinawa kafin a saƙa shi, kuma kada ta sa kwalli a ido dan yin ado, kada ta shafa tirare mai ƙanshi da waninsu, sai dai idan ta yi wankan haila, sai ta shafa wani gutsire ƙarami na tiraren ƙusɗ ko azafar, su wasu nau’uka ne sanannu na tiraren wuta, basu zama daga manufar shafa tirare ba, an yi rangwami a cikinsa ga wacce ta yi wankan daukewar al’ada dan kawar da warin da ba'a so, da zata bibiyi gurbin jini da shi a acikin farji ba dan shafa tirare ba.فوائد الحديث
Ma'anar idda (takaba) shi ita ce: Barin ado da abinda yake jan hankali zuwa ga aurenta, to yana wajaba akanta ta nisanci dukkanin kayan ado, da dukkanin tirare, da kwalli, kuma ta nisanci tufafin ado.
Hani daga takabar mace ga mamaci sama da kwana uku, banda mijinta.
Bayanin matsayin miji, dan ba'a yin idda ga waninsa sama da darare uku.
Halaccin kwana uku ko ƙasa da haka, dan yaye baƙin cikin dake cikin rai.
Wajabcin takabar mace ga mijinta wata huɗu da kwana goma, muddin dai bata zama mai ciki ba to iddarta shi ne idan ta haife ɗan dake cikin ciki.
An halatta mata rinannen tufa idan ba na ado ba ne, amma abin lura a sanin haka shi ne a al'adance.
التصنيفات
Idda