إعدادات العرض
:
:
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, godiya taSa ce, kuma Shi Mai iko ne a kan dukkan komai) sau ɗari a cikin yini, yana da abinda ya yi daidai da wuyaye goma, kuma za'a rubuta masa kyakkyawa ɗari, kuma za'a shafe masa mummuna ɗari, kuma za ta kasance tsari daga Shaiɗan a wannan yinin nasa, har sai ya kai maraice, kuma ba wanda zai zo da abin da ya fi wanda ya zo da shi, saidai wanda ya aikata sama da hakan».
الشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya) babu wani abin bauta da cancanta (sai Allah, Shi kaɗai Yake) a cikin UluhiyyarSa da RububiyyarSa da sunayenSa da kuma siffofinSa, (mulki naSa ne) da tasarrufi da kuma jujjuya al'amura gaba ɗayansa, (godiya taSa ce) akan dukkan abinda Ya halicce shi kuma Ya ƙaddara shi, (Shi Mai iko ne akan dukkan komai) ba tare da wani mai hanawa ko mai karewa ba, abinda bai so ba zai kasance ba. Wanda ya faɗi wannan zikirin sau ɗari a yini kuma ya maimaita shi, za'a rubuta masa lada a wurin Allah kamar ya 'yanta wuyaye goma ne, kuma za'a rubuta masa kyakkyawa ɗari da daraja ɗari a cikin aljanna, kuma za'a shafe masa za'a sarayar masa da mummuna ɗari, kuma zasu zame masa tsari da kiyayewa da katanga da hani daga Shaiɗan da halakarwarsa da kuma rinjayensa a wannan yinin nasa har sai ya shiga yammaci ta hanyar faɗauwar rana, kuma wani ba zai zo da mafificin abinda ya zo dashi ba sai dai wanda ya aikata hakan kuma ya ƙari a kansa.فوائد الحديث
Falalar kalmar tauhidi da kuma girman ladanta.
Yalwatar falalar Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ga bayinSa inda Ya shara'anta musu zikiri mai sauƙi ga kowa, kuma Ya jeranta sakamao da gwaggwaɓan lada a kansa.
Da za ce zai faɗi wannan hailalar sama da ɗari a yini, wannan ladan da aka ambata a cikin hadisin zai zama ɗari ne, kuma yana da wani ladan daban akan ƙarin da ya yi, wannan bai zama yana cikin iyankancewar da aka yi hani akan kari a kansa ba, da kuma ƙetare adadinsu, kuma cewa ƙari akansu babu falala a cikinsu koma su ɓata su ba.
Nawawi ya ce: Zahirin bayanin hadisin wannan ladan da aka ambata a cikin hadisin yana samuwa ne ga wanda ya faɗi wannan hailalar sau ɗari a cikin yininsa, daidai ne ya faɗeta ne a jere ko a rarrabe a zama daya ne ko sashinsu, a farkon yini wani sashin kuma a ƙarshensa, sai dai abinda ya fi ya zo da su a jere a farkon dare, dan ya zama tsari gare shi a dukkanin yininsa.