Qungiyoyi da Mazhabobi tsofaffi Samuwa

Qungiyoyi da Mazhabobi tsofaffi Samuwa

1- Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya aikewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani gutsire na zinare a cikin wata fatar da aka jeme da ƙwallan bagaruwa, ba'a gama tace shi daga ƙasarta ba, ya ce: sai ya raba shi tsakanin mutum huɗu, tsakanin Uyaina ɗan Badr da Aƙra'a ɗan Habis da Zaidul Khail, na huɗun: Ko dai Alƙama ko Amir ɗan Ɗufail, sai wani mutum daga sahabbansa ya ce: Mu mun kasance mu ne mafi cancantar wannan daga waɗannan (mutane huɗun), ya ce: Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: @«Shin bakwa amince mini ba alhali ni ne amintaccen wanda ke sama, labarin sama yana zo mini safiya da yamma"*, ya ce: Sai wani mutum ya mike mai kogon idanuwa, mai manyan kumatu, goshin shi ya yi sama, mai kaurin gemu, mai askakken kai, yana ɗaure da zani, sai ya ce: Ya Manzon Allah ka ji tsoron Allah, ya ce: "Kaicanka, shin ba ni ne nafi cancantar fin kowa tsoron Allah daga mutanen dake ƙasa ba" ya ce: Sannan mutumin ya juya baya, Khalid dan Walida ya ce: Ya Manzon Allah, shin bana daki wuyansa ba? ya ce: "A'a, wataƙila yana sallah" Khalid ya ce: da yawa mai sallar da yake faɗa da harshensa abinda ba ya cikin zuciyarsa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya ce: "Lallai ni ba'a umarceni ba in bibiyi zukatan mutane ba ko na tsaga cikkunansu ba" ya ce: sannan ya yi duba zuwa gare shi alhali shi ya juya baya, sai ya ce: "Lallai cewa wasu mutane zasu fito daga tsatson wannan suna karanta Littafin Allah danye a zuciyarsu, ba ya ketare zukatansu zasu fita daga Addini kamar yadda kibiya take fita ga kwarin da aka harba, ina zatan ya ce: Wallahi idan na riskesu zan kashesu irin kisan Samudawa.