إعدادات العرض
«Wanda ya nemi sanin wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da shi ba ya nemansa sai dan ya samu wata haja ta duniya da shi ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙima»* wato ƙanshinta.
«Wanda ya nemi sanin wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da shi ba ya nemansa sai dan ya samu wata haja ta duniya da shi ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙima»* wato ƙanshinta.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wanda ya nemi sanin wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da shi ba ya nemansa sai dan ya samu wata haja ta duniya da shi ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙima» wato ƙanshinta.
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी Español Kurdî Tiếng Việt Magyar ქართული සිංහල Kiswahili Română অসমীয়া ไทยالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya nemi sanin ilimin shari'a wanda asali a cikinsa shi ne a nufi yardar Allah - Maɗaukakin sarki - da shi ba ya nemansa ba ne kawai sai dan ya samu wani rabo da wani jin daɗi na duniya da shi na dukiya ko alfarma to ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙiyama.فوائد الحديث
Wajabcin ikhlasi a cikin neman ilimi, da kuma kwaɗaitarwa akan hakan.
Gargaɗarwa mai tsanani daga riƙo da ilimin shari'a saboda riya ko abin neman duniya, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.
Cewa wanda ya nemi ilimi saboda Allah - Maɗaukakin sarki - sai duniya ta zo masa dan bi to ya halatta ya karɓeta, hakan ba zai cutar da shi ba.
Sindi ya ce: Faɗinsa (ƙanshin aljanna): ƙanshi, kai matuƙa ne a cikin haramta aljanna; domin cewa duk wanda ba zai ji ƙanshin abu ba to ba zai same shi ba.
Wanda ya koyi wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah da shi saboda neman aiki, ko saboda wasu buƙatu na duniya daban; to wajibi ne ya tuba zuwa ga Allah daga hakan, Allah zai goge masa abinda ya faru na gurɓatacciyar niyya kuma Shi Ma'abocin falala ne Mai girma - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
Wannan gargaɗarwar ga mai neman ilimin shari'a ne, amma wanda ya nemi wani ilimi daga cikin ilimummukan duniya saboda jin daɗin duniya kamar Injiniyarin ko Kimiyya da wasunsu saboda duniya to shi niyyarsa ta tabbata gare shi.