: :

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai cewa Allah idan Ya so wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce: Lallai cewa Ni ina son wane to ka so shi, ya ce: Sai Jibril yaso shi, sannan ya yi kira a cikin sama sai ya ce: Lallai Allah Ya na son wane to kuso shi, sai waɗanda ke sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a cikin ƙasa. Idan kuma Ya ƙi wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce; Lallai Ni ina ƙin wane to ka ƙi shi, ya ce sai (Mala’ika) Jibril ya ƙi shi, sannan sai ya yi kira a cikin waɗanda ke cikin sama lallai cewa Allah Yana ƙin wane to ku ƙishi, ya ce: Sai su ƙishi, sannan a sanya masa baƙin jini a cikin ƙasa».

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya labarta cewa Allah idan Ya so bawanSa mumini; mai biyayya ga umarninSa mai nisantar hane-hanenSa sai Ya kira (Mala’ika) Jibril: Lallai cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana son wane to ka so shi. Sai shugaban mala'iku (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya so shi, sai Jibril yayi kira a cikin mala'ikun sama: Lallai cewa Ubangijinku Yana son wane to ku so shi, sai waɗanda ke sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a cikin zukatan muminai da soyayya da kuma karkata gare shi da kuma yarda da shi. Idan Allah Ya ki wani bawanSa sai Ya kira Jibril: Lallai cewa Ni ina ƙin wane to ka ƙi shi, sai (Mala’ika) Jibril ya ƙishi, sannan Jibril yayi kira a cikin waɗanda ke cikin sama: Lallai Ubangijinku Yana ƙin wane to ku ƙishi; sai su ƙishi, sannan a sanya masa baƙin jini da ƙiyayya a cikin zukatan muminai.

فوائد الحديث

Abu Muhammad Ibnu Abi Jamrah ya ce: A cikin gabatar da umarni da hakan ga (mala'ika) Jibril kafin waninsa cikin mala'iku akwai bayyanar da girman matsayinsa a wurin Allah - Maɗaukakin sarki - akan waninsa daga cikinsu.

Wanda Allah Ya so shi to halittun dake cikin sama da ƙasa zasu so shi, wanda Allah Ya ƙishi to halittun dake cikin sama da ƙasa zasu ƙishi.

Sindi ya ce: Faɗinsa (za'a sanya masa karɓuwa a cikin ƙasa), ba ya lazimtar gamewa, kai hakan akan gwargwadan abinda Allah Ya yi nufi ne na karɓuwa a doron ƙasa, ta yaya alhali ƙiyayyar mutanen banza ga zaɓaɓɓun mtane sananniya ce.

Kwaɗaitarwa akan cika ayyukan alheri akan saɓanin nau'ikansu farillansu da sunnoninsu, da kuma gargaɗarwa daga saɓo da kuma bidi'o'i; domin cewa su masu sabbaba zato ne na fushi.

Ibnu Hajar ya ce: Kuma ana fahimta daga gare shi cewa soyayyar zukatan mutane alamar soyayyar Allah ce, abinda ke cikin jana’iza yana ƙarfafa shi: "Kune shaidun Allah a doron ƙasa".

Ibnul Arabi al-Malaki ya ce: Kawai ana nufi da waɗanda ke cikin ƙasa wanda ya san shi daga cikinsu ne kawai banda wanda bai san shi ba, baima taɓa jinsa ba.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi