1- Cewa mahaifiyarsa 'yar Rawaha ta tambayi babansa wata kyauta daga dukiyarsa ya bawa ɗanta, sai ya jinkirtata shekara sannan ya ga (ya kamata ya yi kyautar), sai ta ce: Ba zan yarda ba har sai ka sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shaida ga abinda ka bawa ɗana kyauta, sai babana ya riƙe hannuna, a wannan lokacin ina yaro, sai ya zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa babar wannan 'yar Rawaha tana son in saka shaida a kan abinda na bawa ɗana kyauta, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya kai Bashir, shin kana da wani dan ne banda wannan?" ya ce: Eh, sai ya ce: "Shin dukkansu ka basu kwatankwacin wannan?" ya ce: A'a, ya ce: @"To kada ka sani shaida, domin cewa ni bana yin shaida akan zalinci"*, A Muslim: "To kasa wani shaida akan wannan ba ni ba".