إعدادات العرض
«Yayin da (Mala’ika) Jibrilu yake zaune a wurin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wata ƙara daga samansa, sai ya ɗaga kansa sama, sai ya ce: Wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, ba'a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai wani Mala'ika ya sauko daga…
«Yayin da (Mala’ika) Jibrilu yake zaune a wurin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wata ƙara daga samansa, sai ya ɗaga kansa sama, sai ya ce: Wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, ba'a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai wani Mala'ika ya sauko daga cikinta, sai ya ce: Wannan wani Mala'ika ne da ya sauko ƙasa, kuma bai taɓa sakkowa ba sai yau, sai ya yi sallama, ya ce: @Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: «Yayin da (Mala’ika) Jibrilu yake zaune a wurin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wata ƙara daga samansa, sai ya ɗaga kansa sama, sai ya ce: Wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, ba'a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai wani Mala'ika ya sauko daga cikinta, sai ya ce: Wannan wani Mala'ika ne da ya sauko ƙasa, kuma bai taɓa sakkowa ba sai yau, sai ya yi sallama, ya ce: Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi».
الترجمة
العربية Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Tiếng Việt Magyar ქართული Kiswahili සිංහල Română অসমীয়া ไทยالشرح
Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya kasance a zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wata ƙara daga sama kamar ƙarar ƙofar da aka buɗe, sai Mala’ika Jibril ya ɗaga kansa da idansa zuwa sama, sannan ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, kuma ba'a taɓa buɗeta ba sai yau ɗin nan, sai wani mala'ika daga cikin mala'iku ya sauko daga gareta zuwa ƙasa, bai taɓa sauka ba kafin nan sai yau, sai mala'ikan ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, kuma ya ce da shi: Ina maka bushara da haske biyu waɗanda aka baka ba'a taɓa bawa wani Annabi kafinka ba; sune: Suratul Fatiha, da kuma ƙarshen ayoyi biyu na Suratul Baƙara. Sannan mala'ikan ya ce: Wani ba zai karanta wani harafi daga garesu ba sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ba shi abinda ke cikinsu na alheri da addu'a da kuma abin da yake nema.فوائد الحديث
Falalar Suratul Fatiha da ƙarshen Suratul Baƙara, da kuma kwaɗaitarwa akan karanta su da aiki da abinda ke cikinsu.
Sama tana da ƙofofi waɗanda umarnin Ubangiji yake sauka daga garesu, kuma ba'a buɗesu sai da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Bayanin girman Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurin UbangijinSa, inda Ya girmama shi da abinda bai taɓa girmama Annabawan dake gabaninsa ba, sai Ya ba shi waɗannan haske biyun.
Daga tsarin kira zuwa ga Allah yin bushara ta alheri.