إعدادات العرض
1- A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: @"Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".
2- Na kasance ina shayar da mutane ( giya) a gidan Abu Ɗalha, kuma giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, sai a (Cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yan dabino kafin su zama ɗanye) Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wani mai kira ya yi kira: @Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata*, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai ta kwaranya a lungunan Madina, sai wasu cikin mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe wasu mutane alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi ga waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka ɗanɗana} [al-Ma'ida: 93] karanta ayar har ƙarshenta.