Falalar Tauhidi

Falalar Tauhidi

5- "Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama*, sai Ya bude masa fayil dinsa x asa'in da tara, kowanne fayil tamkar iya ganinka ne, sannan Ya ce: Shin kana musun wani abu daga wannan? Shin marubutaNa masu kiyayewa sun zalinceka ne? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai Ya ce: Shin kana da wani hanzari? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai (Ubangiji) Ya ce: Eh, lallai kanada wani abu kyakkyawa a wurinmu, a yau babu wani zalinci akanka, sai a fitar da wani kati a cikinsa akwai: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, sai ya ce: ka zo wajan ma'aninka, sai ya ce; ya Ubangiji wannan wanne katine tare da wadannan fayilillikan? Sai Ya ce; Lallai cewa kai ba za’a zalinceka ba, sai ya ce: Sai a dora fayilillikan a bangaren ma'auni , katin kuma a daya ma'aunin, sai fayililliakn su yi sauki, kuma katin ya yi nauyi, wani abu ba zai yi nauyi tare da sunan Allah ba".