Aqida - الصفحة 4
65- Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya aikewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani gutsire na zinare a cikin wata fatar da aka jeme da ƙwallan bagaruwa, ba'a gama tace shi daga ƙasarta ba, ya ce: sai ya raba shi tsakanin mutum huɗu, tsakanin Uyaina ɗan Badr da Aƙra'a ɗan Habis da Zaidul Khail, na huɗun: Ko dai Alƙama ko Amir ɗan Ɗufail, sai wani mutum daga sahabbansa ya ce: Mu mun kasance mu ne mafi cancantar wannan daga waɗannan (mutane huɗun), ya ce: Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: @«Shin bakwa amince mini ba alhali ni ne amintaccen wanda ke sama, labarin sama yana zo mini safiya da yamma"*, ya ce: Sai wani mutum ya mike mai kogon idanuwa, mai manyan kumatu, goshin shi ya yi sama, mai kaurin gemu, mai askakken kai, yana ɗaure da zani, sai ya ce: Ya Manzon Allah ka ji tsoron Allah, ya ce: "Kaicanka, shin ba ni ne nafi cancantar fin kowa tsoron Allah daga mutanen dake ƙasa ba" ya ce: Sannan mutumin ya juya baya, Khalid dan Walida ya ce: Ya Manzon Allah, shin bana daki wuyansa ba? ya ce: "A'a, wataƙila yana sallah" Khalid ya ce: da yawa mai sallar da yake faɗa da harshensa abinda ba ya cikin zuciyarsa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya ce: "Lallai ni ba'a umarceni ba in bibiyi zukatan mutane ba ko na tsaga cikkunansu ba" ya ce: sannan ya yi duba zuwa gare shi alhali shi ya juya baya, sai ya ce: "Lallai cewa wasu mutane zasu fito daga tsatson wannan suna karanta Littafin Allah danye a zuciyarsu, ba ya ketare zukatansu zasu fita daga Addini kamar yadda kibiya take fita ga kwarin da aka harba, ina zatan ya ce: Wallahi idan na riskesu zan kashesu irin kisan Samudawa.
67- "Ni ne shugaban mutane a ranar alƙiyama, shin kun san daga menene hakan? @Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba*, sai mutane su ce: Shin bakwa ganin abinda haƙiƙa ya kai muku ? shin bakwa duba wanda zai yi muku ceto zuwa ga Ubangijinku ba? sai wasu daga mutane su ce wa wasu: Ku je gurin (annabi) Adam, sai su zo wa Adam - aminci ya tabbata agare shi - sai su ce masa: Kai ne uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya busa maka daga ranSa, kuma Ya umarci mala'iku sai suka yi maka sujjada, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana? sai Adam ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushi a yau bai taba irin wannan fushin ba, kuma ba zai taba yin irin wannan fushin ba, kuma lallai ni hakika Ya hanani daga bishiya sai na saba maSa, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Nuhu.
Sai su zo wa (annabi) Nuhu sai su ce: kai Nuhu, lallai kai ne farkon manzanni zuwa mutanen kasa, hakika Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana, shin baka nema mana ceto ga Ubangijinka ba? sai ya ce: Lallai Ubangijina Ya yi fushi a yau bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba, kuma lallai cewa ni akwai mummunar addu'ar da na yi akan mutanena, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi gurin (annabi) Ibrahim.
Sai su zo wa (annabi) Ibrahim sai su ce: kai Ibrahim, kai ne Annabin Allah kuma badaɗayinSa daga mutanen ƙasa, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce musu: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba irinsa, lallai cewa ni na yi ƙarya sau uku, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga (annabi) Musa.
Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai Musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijnka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai ni naa kashe wani rai da ba'a yi umarni da in kasheta ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Isa.
Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: kai Isa, kaine Manzon Allah kuma kalmarSa da ya jefata zuwa Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfidar goyo, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai Isa ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, ba zai anbaci wani zunubi ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -".
Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce kai ne Manzon Allah kuma cika makin Annabawa, hakika Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai in tafi, sai in zo ƙarƙashin al’arshi sai infaɗi ina mai sujjada ga Ubangina, sannan Allah Ya buɗe mini daga godiyarSa da kyakkyawan yabo gareShi na wani abinda bai taɓa buɗewa wani a gabani na ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka shi, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in dago kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Uabngiji, sai ace: Ya Muhammad ka shigar daga al'ummarka wadanda babu wani hisabi akansu ta kofar dama daga kofofin aljanna, kuma su suna tarayya da mutane a koma bayan haka na kofofi".
sannan ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lalai tsakanin ginshikai biyu daga ginshikan aljanna kamar tsakanin Makka ne da Hajar, ko tsakanin Makka ne da Busra".
69- «Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sannan masu biye musu akan surar tauraro mafi tsananin haske*, ba sa fitsari ba sa bahaya, ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abin taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski, kuma abin kunna tiraren wutarsu shi ne icen tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inun (Masu tsananin farin ido da tsananin ƙwayar baƙin da ke cikin idon), suna a kan halittar mutum ɗaya, akan surar babansu (Annabi) Adam, zira'i sittin a cikin sama».