Aqida - الصفحة 2

Aqida - الصفحة 2

1- Wani mutum daga mutanen Najad ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai dattin kai, muna jin ƙarfin muryarsa, ba ma fahimtar abinda yake faɗa har ya kusanto ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai gashi yana tambaya game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Salloli biyar a yini da dare" sai ya ce: Shin akwai wasu kuma akaina? ya ce: "A'a, sai dai idan ka yi nafila. Da azumin Ramadan”. Sai ya ce: Shin akwai wani kuma?. sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Saidai idan ka yi na nafila. Sai ya ambata masa zakka, sai ya ce: Shin akaina akwai waninta ? ya ce: "A'a, saidai idan ka yi nafila", ya ce: Sai mutumin ya juya baya, yana cewa: Na rantse da Allah, ba zan kara akan wannan ba, kuma ba zan rage daga gare su ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce@ ya rabauta idan gasgata hakan".

11- Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, sai ya ce: @"Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa*, ka bautawa Allah kada ka yi shirka da komai da Shi, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin Allah”, sannan ya ce: "Shin ba na shiryar dakai ba ga ƙofofin alheri: Azimi garkuwa ne, sadaka tana kashe kuskure kamar yanda ruwa yake kashe wuta, da sallar mutum a tsakiyar dare" ya ce: Sannan ya karanta: "{Sasanninsu suna nisanta daga makwantansu}, har yakai {Suke aikatawa}". Sannan ya ce: "Shin bana baka labari da asalin al'amari gaba dayansa ba da ginshikinsa, da kololuwar tozansa?" Na ce: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: "Asalin al'amari Musulunci, kuma ginshikinsa sallah, kuma kololuwar tozansa Jihadi" sannan ya ce: "Shin bana baka labari da abinda zai tattaro hakan gaba dayansa ba?" na ce: Eh, Ya Manzon Allah, sai ya rike harshensa ya ce: "Ka rike wannan", na ce Shin za’a kama mu da abinda muke magana da shi? ya ce: "Babarka ta yi wabinka ya Mu'az, ai ba wani abu ne yake afka mutane cikin wuta ta fuskokinsu ko ta hancinansu ba sai abinda harasansu suke girba".

60- Mun kasance muna zaune a gefen manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, a tare damu akwai Abubakar, da Umar a cikin wasu mutane, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe a tsakaninmu, sai ya ɗan jikirta mana, sai muka ji tsoron a cutar da shi ba mu sani ba, sai muka firgita, sai muka tashi, na kasance farkon wanda ya firgita, sai na fita ina neman manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - har na zo wani shinge na mutanen Madina na Banu Najjar, sai na kewaye shi shin zan samu wata ƙofa gare shi ? ban samu ba, sai ga wata 'yar ƙorama tana shiga a cikin shingen daga rijiyar Kharija - rabi'u shi ne korama - sai na takure, sai na shiga wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi -, sai ya ce: "Abu Huraira" sai na ce: Eh, ya manzon Allah, ya ce: "Meke tafe da kai?" na ce: Ka kasance a tsakaninmu, sai ka miƙe, sai ka jinkirta gare mu, sai muka ji tsoron a cutar da kai bamu sani ba, sai muka firgita, sai na zama farkon wanda ya firgita, sai na zo wannan shingen, sai na takure kamar yadda dila yake takurewa, alhali waɗannan mutanen suna bayana, sai ya ce: "Ya Abu Huraira" sai ya bani takalmansa, ya ce: @"Ka tafi da takalman nan waɗannan, duk wanda ka gamu da shi ta bayan wannan shingen yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma zuciyarsa tana sakankancewa da ita, to ka yi masa albishir da aljanna"*, sai Umar ya zama farkon wanda ya haɗu da ni, sai ya ce: Waɗannan takalman fa ya Abu Huraira? sai na ce: Waɗannan takalman manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya aikoni da su cewa wanda na haɗu da shi yana shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da ita, in yi masa albishir da aljanna, sai Umar ya daki tsakanin nonuwana da hannunsa sai na faɗi ta bayana, sai ya ce: Ka koma ya Abu Huraira, sai na koma wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai na fara shesseƙin kuka, kuma Umar ya hauni, sai gashi a bayana, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Meke damunka ya Abu Huraira?" na ce: Na hadu da Umar, sai na ba shi labarin abinda ka aikoni da shi, sai ya daki tsakanin nonuwana duka da na fadi ta bayana, ya ce: Ka koma, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya Umar, me yasa ka aikata haka?" ya ce: Ya Manzon Allah, fansarka babana da babata, shin ka aiki Abu Huraira da takalmanka cewa idan ya gamu da wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da ita ya yi masa albishir da aljanna? ya ce: Eh, ya ce: Kada ka aikata, domin cewa ni ina jin tsoron mutane su dogara a kanta, kyalesu su yi aiki, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: to ka kyalesu.