Faxakarwa da Wa’azozi

Faxakarwa da Wa’azozi

22- "Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi* - zuwa Aljanna, sai ya ce: ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta sai ya dawo, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa wani daya ba zai ji ta ba sai ya shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan ki, sai Ya ce; Tafi zuwa gareta ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga ta an kewayeta da abubuwan ki, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa shiga cikinta . Ya ce: Tafi ka yi duba zuwaga wuta da kuma abinda na tanada ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga shashininta yana hawa kan sashi, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa ba wanda zai shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan sha'awa , sai ya ce; ka koma ka yi duba zuwa gareta, sai ya yi duba zuwa gareta sai ga shi ita kuma an kewayeta da abubuwan sha’awa, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa tsira daga gareta a ce bai shigeta".

43- Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zauna wata rana akan minbari muma muka zauna a gefensa, sai ya ce: @"Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a buɗe muku na ƙawar duniya da adonta"* sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, shin alheri yana zuwa da sharri ne? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shiru, sai akace masa: Meke damunka ne? kana yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma bai kulaka ba ? sai mukaga cewa can ana saukar me (da wahayi) ne? ya ce: Sai ya shafe gumi daga gare shi , sai ya ce: "Ina mai tambaya?" kamar shi ya yabe shi , sai ya ce: "Lallai alheri ba ya zuwa da sharri, yana daga abinda kaka take tsirarwa (akwai) abinda yake kashewa ko ya aibata, sai masu cin ciyayi, sun ci har saida kwiɓinansu suka cika sai suka fuskanci idan rana, sai suka yi toroso suka yi fitsari, suka yi kiwo, lallai wannan dukiyar koriyace mai zaƙi, madalla da na musulmi abinda aka bawa miskini daga gareta da maraya da ɗan matafiyi - ko kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata ya ce -: Kuma cewa shi wanda ya ɗauketa ba tare da haƙƙinta ba, to kwatankwacinsa kamar wanda yake ci ne ba ya ƙoshi, zata zama mai yi masa shaida ranar alƙiyama".

81- Cewa wani mutum ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah ! ina da bayi biyu suna yi mini karya suna ha'intata suna saba mini, ni kuma ina zaginsu ina dukansu, ya matsayina yake garesu (a urin Allah?) Ya ce: "@Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka yi musu*, idan ukubar da ka yi musu gwargwadan laifinsu ne, ya zama daidai wa daida, babu komai gareka ko akanka. Idan ukubar ka akansu kasa da laifin su ne to ya zama falala gareka, idan ukubarka garesu sama da laifin su ne za’a yi masu sakayyar karin daga gareka", ya ce: Sai mutumin yadan yi nesa sai ya fara kuka yana kururuwa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ba ka karanta littafin Allah ba: {zamu sanya ma'auni na adalci ga yinin Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abu ba}. karanta zuwa karshenta, sai mutumin ya ce; Wallahi ya Manzon Allah, ban ji wani abu gareni dasu ba mafi alheri daga rabuwa da su, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne gaba dayansu.